An kafa sabuwar jam'iyya a Nijar

Akwai jam'iyyun siyasa da dama a Nijar
Bayanan hoto,

Akwai jam'iyyun siyasa da dama a Nijar

A Jamhuriyar Nijar wasu tsofin shugabannin jam'iyar CDS Rahama sun kafa wata sabuwar jam'iyar siyasa mai suna RDR Chanji a takaice.

Shugabanninta na wucin gadi sun ce kamar yadda sunan jam'iyar ya nuna, suna son kawo chanji ne dangane da yadda gwamnatin Mahamadu Isufu ke tafiyar da jagorancin kasar.

Alhaji Falke Basharu shi ne shugaban jam'iyyar, ya yin da Alhaji Ali Mamman da Amadou Lawal da aka fi sa ni da Edmour na daga cikin mataimakansa.

Manufar jam'iyyar kamar yadda shugabannin ta suka ce samun canji a tsarin mulkin da ake yi a jamhuriyar ta Nijar.

Haka kuma an kafa ta ne da nufin samar wa 'yan kasa wata jam'iyyar da za su fake a cikin ta, musamman wadanda suke ganin tsarin mulkin na yanzu baya musu adalci.