Biri ya haddasa mummunan rikici a Libya

Birin
Bayanan hoto,

Birin na wasu mutane daga wata kabila ya abkawa wasu yara mata 'yan makaranta na wata kabila

Jami'ai da masu fafitika a kasar Libya sun ce wani Biri ya haddasa mummunan artabu tsakanin wasu kabilu biyu da ke kasar.

Kawo yanzu babu cikakken bayani game da lamarin, sai dai wasu majiyoyi a jihar Sabha dake kudancin kasar sunce rikici ya barke ne bayan da Birin na wasu mutane daga wata kabila ya abkawa wasu yara mata 'yan makaranta na wata kabila dake yankin.

Hakan dai ya haddasa kashe kashe na ramuwar gayya, lamarin daya kaiga har aka kwashe kwanaki hudu ana bata kashi.

Rahotanni sun ce akalla mutane 16 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wannan rikici da Biri ya haddasa.