Tattalin arzikin Nigeria ya kara samun nakasu

Hada-hada a Lagos

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Farashin kayayyaki sun yi tashin gwauron zabi saboda wannan matsalar

Alkaluman da hukumomi suka fitar sun nuna cewa tattalin arzikin Najeriya ya kara samun nakasu da kashi 2.2 cikin dari a watanni uku da suka gabata.

A bayanin da ta fitar a ranar Litinin, Hukumar kula da kididdiga ta NBC ta ce a bana, karfin tattalin arzikin kasar ya ragu da kashi 2.24 cikin dari.

Ana danganta wannan nakasu ne da karancin kudaden waje da 'yan kasuwa ke fama da shi da kuma hare-haren da masu tayar da kayar baya ke kaiwa a yankin Niger Delta.

Najeriya na fuskantar rikicin tattalin arziki mafi muni a cikin shekaru 20.

Sai dai rahoton ya ce tattalin arzikin ya bunkasa a bangaren da bashi da alaka da man fetur, sannan ana samun ci gaba a fannin noma.

Faduwar darajar mai a kasuwannin duniya ta haifar da karancin kudaden shiga ga kasar, wacce tattalin arzikinta ya dogara a kan man fetur.

Wannan lamari ya haifar da hauhawar farashi da karancin kudaden waje, abin da ya kai ga faduwar darajar kudin kasar - wato naira.

Miliyoyin 'yan kasar na fama da hauhawar farashi mafi girma a cikin sama da shekaru goma.

Wani wakilin BBC a Najeriya ya ce gwamnati za ta yi jin tsoron cewa karuwar marasa ayyukan yi ka iya sa mutane su yi bore.