Nigeria: An bayar da belin mai shari'a Ngwuta kan miliyan 100

Alamar alkalanci
Bayanan hoto,

An dade ana zargin cin hanci a fannin shari'ar Najeriya

Wata babbar kotu a Nigeria ta bayar da belin wani alkalin kotun kolin kasar bayan da ya musanta aikata laifuka 15 da suka hada da halatta kudaden haram da cin hanci.

An bayar da belin Sylvester Ngwuta a kan kudi naira miliyan 100 da kuma kimar da yake da ita.

A zaman kotun na ranar Litinin, lauyoyinsa da na gwamnati sun kai ruwa-rana kan batun belinsa, amma daga bisani alkalin kotun ya amince da bukatar ta sa.

Najeriya ta dauko hayar wani mai gabatar da kara ne dan kasar waje domin ya jagoranci rukunin lauyoyinta.

Za a ci gaba da sauraron karar a ranakun 7, 8 da kuma 9 ga watan Disamba.

Mai shari'a Ngwuta na cikin alkalai bakwai wadanda jami'an tsaro suka kai sumame gidajensu a wani yunkuri na kawar da cin hanci daga bangaren shari'a.

Kungiyar lauyoyi ta kasar ta yi Allah-wadai da matakin da jami'an tsaron suka dauka.

Jami'an tsaron farin kaya na DSS sun kare matakin na su, suna masu cewa "makudan kudaden da suka samu ciki har da na kasashen waje sun nuna yadda alkalan ke aikata ba daidai ba".

Tuni dai hukumar NJC da ke sa ido kan fannin shari'a a kasar ta dakatar da alkalan, wanda suka musanta zargin da ake yi musu.

Wannan ne karon farko da aka gurfanar da wani daga cikin alkalan.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin yaki da cin hanci da rashawa wanda ya yi kasar katutu.