Shirin mata 100 rabin muryar al'umma ya dawo

Mata 100

Masu iya magana na cewa rana ba ta karya, Allah ya kawo mu shekara ta kawo mu.

Bana ma za mu kawo muku shirin mata 100 rabin muryar al'umma kamar yadda muka yi a baya.

A cikin makonnin uku masu zuwa za mu kawo muku rahotanni a kan sauyin da bujirewar mata ya haifar tare da hirrararki da shahararrun mawaka na duniya da wasanni da siyasa har ma da wasu matan wadanda baku sani ba, amma kuma duk suna da labarai masu cike da ban mamaki da nishadantarwa da za su bayar.

Menene shirin mata 100 rabin muryar al'umma

Shirin BBC na mata 100 shiri ne da a duk shekara ke ambato sunayen mata a duniya masu ilhama da kuma fada a ji.

A cikin shirin za mu kawo muku hirarraki da rahontanni domin duba labarai na mata daga sassa daban-daban na duniya.

Me yasa muke yi?

BBC ta samar da shirin mata 100 rabin muryar al'umma ne saboda ta kara yawan mata a cikin shirye-shiryenta da take yi tare da kara yawan mata masu sauraron shirye-shiryen.

Zamu cigaba da yin tambayoyi a kan:

Ya ya rayuwar mata ta kasance a cikin tattalin arzikin karni na 21 a inda kuke?

Shin mata za su samu muhimman matsayi a siyasa da kasuwanci? Ko kuwa dai duniya bata ba su dama ba?

Wadanne ne hadura mafi girma ne mata ke fuskanta? Ya ya batun samun muhimman damarmaki a cikin rayuwa?

Ya matsayinsu yake a kafafen yada labarai? Muna yi wa mata mummunar fasara?

Muna bada labaran da suka shafi mata yadda ya kamata?

Muna so ku kasance tare da mu ta hanyar bayar da shawarwari da yadda kuke kallon al'amura da kuma ra'ayoyinku.

Za ku iya tuntubarmu a shafin Facebook da kuma Instagram. Ku yada manufofinmu a kan shirin mata 100 rabin muryar al'umma ta hanyar rarraba labaranku da maudu'in #100women.

Muna cikin shekara ta hudu, shirin wannan shekarar yafi na bara da aka yi. Ga wasu daga cikin irin abubuwan da za ku sa ran gani:

Asalin hoton, Theo Wargo

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Hira da Alicia Keys, shahararriyar mawakiyar nan, 'yar kasar Amurka a kan bakaken fata a kasar da kuma yadda Amurkar za ta kasance bayan Obama ya sauka daga mulki da kuma kafin Trump ya karbi mulki a kasar.

A cikin hirar za kuma a tattauna abubuwan da suka shafi mata, da kwalliya da shahara da bujirewa tare da tarbiyyantar da yara maza.

Shirin BBC na mata 100 rabin muryar al'umma zai shirya bikin nuna al'adu a birnin Mexico inda za a yi wake-wake da zane da raye-raye da kuma muhawara.

Taron zai bayyana labaran mata wadanda aka ceto kuma za mu nuna muku wadannan labarai ne ta sigar zane wanda zai bai wa mai kallo damar kasancewa cikin labarin wata mata wadda wata kungiya ta yi safararta kuma za a ceto ta.

A watan Yuli ne wata matashiya wace ta ke sanye da doguwar riga mai fadi da hannayenta a nade ta tsaya a gaban wasu 'yan sanda masu dauke da makamai tana kallon kasa.

Iesha Evans ce matar da ke cikin hoton da ya shahara. Ta yi mana karin bayani a kan zanga-zanga da kuma juriya.

Asalin hoton, JONATHAN BACHMAN

Iesha na cikin shirinmu na mata biyar masu bujirewa tsammani da iyakoki a sassan duniya baki daya.

A wata hira ta musamman da za mu yi, za mu tattauna a kan tambayar da ta shafi mata: Ko duka mata ne suke goyon bayan bukatar mace ta samu daidaito da maza?

Kimberle Williams Crenchaw, Heather Rabbatts da Gail Lewis sun duba ko mata sun yi nasarar samun daidaito da maza ta hanyar hada kan mata daga kabila da yaruka daban daban.

Bari mu gabatar muku da mahaifiyar bishiyoyi. Mun ziyarci wata mata mai shekara 105 wace ba ta taba haihuwa ba, amma kuma ta shuka tare da kula da daruruwan bishiyoyi a wasu kauyuka a kasar Indiya.

Za mu kawo karshen shirinmu na mata 100 rabin muryar al'umma na wannan shekarar da tambayar: Ko intanet na nuna fifikon jinsi?

Shafin Wikipedia na intanet shi ne shafin da aka fi sani a duniya, amma kashi 15 cikin 100 na mutanen da ke gyare-gyare ne kawai mata kuma yawan matan da ke da bayanan su a kan Wikipedia ba su kai kashi 15 cikin 100 ba.

Za mu yi aikin sa'oi 12 da Wikipedia domin karfafawa mata da dama gwiwar yin gyare-gyare da kuma kara yawan bayanai da labarai da suka shafi mata a shafin.

A ranar 8 ga watan Disamba, muna so ku kasance tare da mu a shafinmu na BBChausa.com da kuma #100womenwiki domin koyon yadda ake gyare-gyare a Wikipedia.