Harin bam ya kashe 'yan Shi'a da dama a Afghanistan

Masallaci a Afghanistan

Asalin hoton, Reuters

Yan sanda a Afghanistan sun ce akalla mutum 27 ne suka mutu a harin kunar bakin wake da aka kai a cikin wani masallacin 'yan Shi'a a birnin Kabul.

Akalla wasu mutum 35 kuma sun samu raunuka a harin wanda aka kai a masallacin Baqir ul Olum da ke yammacin birnin.

Wani dan kunar bakin wake ne ya tara da bam din da ke jikinsa a lokacin da masallacin ya cika da wadanda ke halartar tarurrukan addu'o'i na musamman.

Kungiyar masu ikirarin kafa daular Musulunci ta IS ta ce ita ta kai harin.

Wakiliyar BBC a birnin ta ce wasu mazauna unguwar sun ce sun ga gawarwaki da dama, yayin da wasu rahotanni suka ce yara kanana na cikin wadanda suka mutu.

Ana kuma fargabar cewa watakila a samu karuwar a adadin mutanen da suka rasu a harin.

Harin na ranar Litinin ya zo ne a lokacin da ake shirin tunawa da Iman Hussaini, jikan Annabi Muhammad (SAW).

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An kai wadanda suka jikkata asibiti

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Takalman wadanda harin ya ritsa da su