Ban san adadin dukiyar da na mallaka ba - Saraki

Bayanan sauti

Ban san adadin dukiyar da na mallaka ba - Bukola Saraki

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya shaida wa BBC cewa bai san adadin dukiyar da ya mallaka ba, amma ya ce ya samu kashi 95% na dukiyar ne kafin ya shiga siyasa.

Sai dai bayanan da kotun kula da da'ar ma'aikata ta fitar sun nuna cewa ya mallaki dimbin dukiya da kadarori a ciki da wajen kasar.

Sanata Saraki na fuskantar shari'a kan zargin yin karya a kadarorin da ya bayyana kafin ya zama gwamnan jihar Kwara a shekarar 2003, lamarin da ya musanta.

Ya shaida wa Naziru Mikailu cewa akwai cin hanci a Najeriya, amma ya ce ya tara dukiyarsa ne saboda daukakar da Allah ya yi wa iyayensa da kuma kwazonsa.

Sannan ya ce yana da kwarin gwiwa cewa zai wanke kansa a shari'ar da ake yi masa, domin cigaba da zama a kan karagar mulki.

Tsohon gwamnan na jihar kwara ya kuma bai taba kaucewa biyan haraji ba - zargin da ya taso a takardun bincike na masu kaucewa biyan haraji wato Panama Papers.

An ambaci sunan matarsa a bayanan inda aka zarge ta yin rijistar wani kamfani a kasar waje domin sayen gida a birnin London.

Wasu daga cikin tambayoyin da Naziru Mikailu ya yi wa Saraki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bukola Saraki na daya daga cikin 'yan siyasar da suke da karfin iko a Najeriya

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

NAZIRU: An dade ana magana a kan batun cin hanci da rashawa, ko ka amince cewa cin hanci yayi wa Najeriya katutu?

SARAKI:Hankalina ya koma ne ga batun cewa hakika akwai matsalolin da suka kamata a warware, amma ba zan yi ta jaddada hakan ba. Saboda ni ma ina tallata kasata ne, don in sami shigowar 'yan kasuwa masu zuba jari. Shi ya sa ya zama wajibi in samar da wani yanayi da ya dace wanda zai karfafa hakan, don in babu hakan, don gwamnati ita kadai, zai yi wuya mu sami ci gaban da muke bukata.

NAZIRU: Ko ka ga ana aikata cin hanci a harkokin gwamnati?

SARAKI:Tabbas, akwai matsala, shi ya sa ma muke da aikin sa ido kan gudanar ayyuka. Kamar sauran wasu kasashen duniya da dama, mu ma muna da ire-iren wadannan matsaloli. Amma dai ina ganin mun yi nisa wajen shawo kan matsalar.

NAZIRU: Mutane da dama a kasar nan na yi wa 'yan siyasa kallon masu kudi - shin kai nawa ka mallaka a rayuwarka?

SARAKI: Ban sani ba.

NAZIRU: Nawa ka bayyana a matsayin kadararka kafin ka shiga siyasa?

SARAKI: A zamana nan ba na iya tuna alkaluman da na gabatar.

NAZIRU: Wannan na nufin cewa makudan kudade ne ke nan?

SARAKI: Ba na jin laifi ne a ko'ina a ko dai ka yi aiki tukuru ko kuma Allah Ya albarkace ka, ka sami arziki. Amma dai abin da nake gani muhimmi shi ne sadaukarwarka ta yi wa jama'a aiki.

NAZIRU: Ta yaya ka mallaki wannan dinbin dunkiya?

SARAKI: Na fito ne daga iyalin da Allah Ya yi wa albarka ta arziki. Iyayena sun samu dama a rayuwarsu, kuma kafin nan ma na yi fadi-tashi a harkokin kasuwanci. Ina ganin na yi aiki da gumina, na mallaki duk abin da nake da shi. Je ka duba dukiyata, kashi casa'in da biyar cikin na mallake ta ne tun kafin in shiga gwamnati.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bukola Saraki ya ce siyasa ce ta sa ake yi mana wannan shari'ar

NAZIRU: Ka yi magana akan tara kudaden shiga da karbar haraji, amma sai ga shi an ambato daya daga cikin iyalanka a takardun bincike na masu kaucewa biyan haraji wato Panama Papers?

SARAKI: Wannan batu ne na kafa wani kamfani, amma babu wani da ake da alaka da batun biyan haraji.

NAZIRU: To amma mai yasa aka kafa kamfanin?

SARAKI:An yi hakan ne bisa shawarwarin lauyoyi, saboda za a sayi wata kadara, kuma ita ce shawarar da aka bayar a wancan lokacin. Ba wai kamfani ne da muka kafa da kanmu ba, a'a, lauyoyi ne suka kafa, kuma a iya saninmu babu wata doka da aka keta.

NAZIRU: Kana fuskantar shari'a a yanzu haka inda ake zarginka da yin karya wurin bayyana kadarorinka?

SARAKI:Wannan haka yake, kuma ana ci gaba da wannan shari'a.

NAZIRU: Ko ka bayyana wata kadara da ba ka mallaka ba?

SARAKI:Kamar yadda na dade ina fada game da wannan shari'a, zan wanke kaina, zan tabbatar da cewa ban aikata laifi ba. Wadannan takardu ne da na cike tun shekaru sha uku da suka wuce, amma ba a taso da batun ba, sai a watan Agusta bayan da na zama shugaban majalisar dattawa. Da ace akwai wani kuskure a ciki, da kamata ya yi kotun kula da da'ar ma'aikatan ta yi magana a kai, amma ba su yi ba. Don haka, kamar yadda na fada, ina da kwaarin gwiwar wanke kaina, domin babu wani laifi da na aikata.