Mutanen da aka yiwa kawanya a Syria sun karu- O'Brien

Mutane kusan miliyan guda ne aka yiwa kawanya

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mutane kusan miliyan guda ne aka yiwa kawanya

Majalisar dinkin duniya ta ce adadin al'ummar Syria da ke rayuwa cikin kawanya ya rubanya na wanda ake da shi a watanni shida da suka gabata inda ya kusa kaiwa miliyan guda.

Mafi yawan wadanda aka yiwa kawanyan dai na karkashin dakarun gwamnatin kasar ne, kuma an ware su, ga yunwa ga hare-haren bama-bamai da ake kaiwa, sannan kuma an hana akai musu taimakon magani.

Shugaban ayyukan jin kai na majalisar, Stephen O'Brien ya ce yakamata kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya dauki kwakkwaran mataki na kawo karshen hare-haren da ake kaiwa fararen hula, sannan kuma a bude hanyoyin kai kayan gaji.

Har yanzu yunkurin kasashen duniya na samar da zaman lafiya a Syria ya ci tura duk da irin asarar rayukan da ake yi.

Hakan dai na da nasaba ne da yadda manyan kasashe ke goyon bayan bangarori daban-daban a rikicin.

Lamarin da ke kara jefa fararan hula cikin mawuyacin hali.