Za a kawo karshen matsalar yajin aikin likitoci a Nijar

Kungiyar kwararrun likitocin ta Nijar ta shafe shekaru biyu ta na yajin aiki jefi-jefi
Bayanan hoto,

Kungiyar kwararrun likitocin ta Nijar ta shafe shekaru biyu ta na yajin aiki jefi-jefi

A jamhuriyar Nijar, majalisar dokokin kasar ta gayyaci ministan kiwon lafiya domin ya yi musu bayani a kan yaje-yajen aikin da kungiyar kwararrun likitoci ke yi.

Fatan gayyatar dai ita ce duba matakan da suka dace a dauka domin shawo kan matsalar.

Da ya bayyana gaban majalisar, ministan kiwon lafiyar,Dakta Iliyasu Idi Mai Nasara ya tabbatar da cewa gwamnati ta yi iya bakin kokarinta a shekarun baya-bayan nan wajen kyautata yanayin aikin jami'an kiwon lafiya da saka kwararrun likitocin cikin hali na gari musamman kyautata albashinsu, dan haka yajin aikin da kungiyar kwararrun likitocin ke yi ba shi da hujja.

Kungiyar kwararrun likitocin ta SMES ta kwashe sama da shekaru 2 ta na yajin aiki jefi-jefi da zummar tilasta wa gwamnati ta kara wa 'ya'yanta albashi da wasu alawus-alawus ba tare da ta samu biyan bukata ba.