'IS na amfani da makaman Amurka da Sa'udiyya'

Mayakan IS
Bayanan hoto,

Rahoton ya dora alhakin hakan kan yamutsin da ake ciki a fagen daga a kasashen Syria da Iraki.

Wasu masu bincike sun ce sun gano cewa kungiyar IS na amfani da makamai da kuma albarussan da gwamnatocin Amurka da Sa'udiyya suka sayo.

Masu binciken na kungiyar Conflict Armament Research sun ce an samu makaman da aka kera a gabashin Turai a wasu yankunan kasar Iraki da aka kwato daga kungiyar ta IS.

An yi niyyar kai makaman ne ga 'yan tawayen da ke fada da sojojin gwamnati a Syria amma saboda wasu dalilai aka karkata akalarsu zuwa ga mayakan IS.

Masu binciken sun yi kira ga masu kera makaman da masu sayen su da su mayar da hankali kan yadda ake shawagi da makaman.