Ana tuhumar tsohon dan wasan NBA, Rodman da tukin ganganci

Dennis Rodman da Micheal Jordan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rodman ya dauki kofin gasar NBA uku da Chicago Bulls tare da Micheal Jordan

Ana tuhumar tsohon dan wasan kwallon kwando na gasar NBA ta Amurka Dennis Rodman da laifin tukin ganganci da guduwa bayan haddasa hadari, wanda hukuncinsa zaman kurkuku ne na shekara biyu.

An zargi Rodman mai shekara 55 da bin hannun da ba nasa ba a titin kudancin California, lamarin da ya sa wani mai mota ya yi karo da kankaren gefen titi a kokarin kauce masa.

Masu gabatar da kara sun ce Rodman ya gudu bayan da ya haddasa hadarin, a ranar 20 ga watan Yuli, kuma ya ba wa 'yan sanda bayanan karya.

An kuma tuhume shi da laifin tuki da lasisin da ya kare aiki.

Lauyan Rodman Paul Meyer, ya ce lamarin ya faru ne a titin da ba a yi masa alama mai kyau ba da direbobi za su gane.

Kuma ya ce tsohon dan wasan ya gyara kuskuren tukinsa, inda ya kauce wa daya motar ba su yi karo ba, sannan ya tsaya ya yi wa wadanda ke cikin daya motar magana.

Ranar 20 ga watan Janairu ne za a zauna shari'ar.

Rodman ya dauki kofi biyu da kungiyar Detroit Pistons da kuma wasu kofunan uku da fitacciyar kungiyar nan ta Chicago Bulls a tsakiyar shekarun 1990 tare da Michael Jordan.