CAF ta fitar da sunayen gasar gwarzon dan kwallon Afirka

Pierre Emerick Aubameyang, Yaya Toure
Bayanan hoto,

Pierre Emerick Aubameyang ne ya samu kambun gwarzon dan kwallon Afirka na CAF na 2015

Hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF, ta fitar da sunayen 'yan wasa biyar da a cikinsu za a zabi gwarzon dan wasan Afirka na 2016.

Dan wasan Gabon na Borussia Dortmand, Pierre Emerick Aubameyang, wanda ke rike da kambun na da damar komawa da shi gida.

Sai dai kuma yana fuskantar hamayya daga 'yan wasan Algeria biyu Riyad Mahrez, da Islam Slimani.

Sauran 'yan wasan biyu da ke cikin jerin su ne Senegal Sadio Mane da Mohammed Salah na Masar, wanda ke jan zarensa a kungiyarsa ta Italiya, Roma.

A ranar 12 ga watan Disamba ne za a bayyana Gwarzon dan wasan kwallon kafar Afirka na BBC na wannan shekara ta 2016, wanda a yanzu masu sha'awa ke ci gaba da kada kuri'arsu kan gwanin da suke so.

A gasar ta BBC dai akwai 'yan wasan Afirka guda biyar Pierre emerick-Aubameyang da Yaya Toure da Sadio Mane da Riyad Mahrez da kuma Andre Ayew