Trump ya nada mai sukarsa Nikki a matsayin jakadiyar Amurka a MDD

Trump ya nada Nikki Haley a cikin tawagarsa

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Matashiyar Gwamnar South Carolina, Nikki Haley

Tawagar Donald Trump ta sanar da nada Gwamnar South Carolina, Nikki Haley, a matsayin jakadiyar Amurka a Majalisar dinkin duniya.

Ita ce mace ta farko da ba farar fata ba da tawagar Trump ta nada domin yin aiki tare.

Mrs Haley 'yar ci-rani ce wadda ta dinga sukar Trump a lokacin da yake yakin neman zabe.

Ana alakanta Haley, mai shekara 44, da wadda tauraruwarta take haskawa a jam'iyar Republican wadda ake cewa ita ce gwamna mafi karancin shekaru.

Koda yake ta zabi Mr Trump a lokacin zabe, amma ta ce shugaban da Hillary dukkansu ba mutanenta ba ne.

Tun farko Mrs Haley ta zabi Marco Rubio, Sanatan Florida, a lokacin zaben fitar da gwani na jam'iyar Republican, daga baya ta marawa Senata Ted Cruz baya.