Jirgin sama ya yi hadari da 'yan kwallon Brazil

Hadarin jirgi a Colombia

Asalin hoton, MI ORIENTE

Bayanan hoto,

Ta kasa ne kawai masu aikin ceto za su iya kai wa wurin da lamarin ya faru

Wani jirgin sama dauke da mutum 81, ciki har da kulob din kwallon kafa na Brazil, ya fadi a kusa da birnin Medellin na kasar Colombia.

Rahotanni sun ce akalla mutum shida ne suka tsira. Jirgin ya samu matsalar na'ura ne.

Jami'an filin saukar jiragen sama sun ce jirgin, wanda aka dauki hayarsa, ya taso ne daga Bolivia yana dauke tawagar 'yan kwallon kulob din Chapecoense.

Tawagar na shirin karawa ne a wasan karshe na Copa Sudamericana tare da kungiyar Atletico Nacional na birnin Medellin.

An tsara za a yi kashi na biyu na wasan karshe na gasar wacce ita ce ta biyu a muhimmanci a Kudancin Amurka a ranar Laraba, amma yanzu an dage ta.

Hukumar kula da kwallon kafa ta Kudancin Amurka (Conmebol) ta ce ta dakatar da dukkan "aikace-aikacenta".