OPEC ta amince ta rage yawan man da take hakowa

Kasashen Opec

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An dade ana kokarin cimma wannan yarjejeniya

Kasashen da ke kungiyar OPEC, masu arzikin man fetur, sun amince su rage yawan man da suke hakowa, a karon farko cikin shekara takwas.

Muhammad Barkindo, babban sakataren kungiyar, ya shaida wa BBC cewa za a fara rage man da ya kai ganga miliyan daya da dubu dari biyu daga watan Janairu.

Bayanan sauti

Kungiyar OPEC

Wannan na zuwa ne bayan sama da shekara ana fama da faduwar farashin, wanda ya ragu da fiye da rabi tun 2014, saboda yawaitarsa a kasuwa.

Farashin mai samfurin Brent ya tashi da kashi 9% zuwa sama da dala 52, yayin da man Amurka kuma ya tashi zuwa dala 50.

Su ma kasashen da ba sa cikin kungiyar ta Opec ana sa ran za su rage adadin da suke hakowa da ganga 600,000 a kowacce rana.

Kasashen Najeriya, Iran da kuma Libya ba za su rage na su adadin man ba saboda wasu matsaloli da suke fama da su.

A watan Satumba ne kungiyar, mai mambobi 14, ta amince ta rage yawan man da take samarwa.

Wannan yarjejeniya ta zo bayan wani taro da su ka yi a Vienna, a kasar Austria, inda bambancin siyasa tsakanin Iran da Saudiyya ya nemi kawo cikas a lamarin.

Hakan dai labari ne mai dadin ji ga kasashe kamar su Najeriya wadanda tattalin arzikinsu yake tangal-tangal saboda faduwar farashin man.