Kasuwanci tsakanin Amurka da China zai dore - Wang Yang

Wang Yang
Bayanan hoto,

Wang Yang ya ce irin sha'awar da 'yan kasuwar Amurka ke da ita ta yin kasuwanci da China ba ta canza ba

Mataimakin firaministan China Wang Yang ya ce ya na da kyakkyawan fata cewa huldar kasuwanci tsakanin Amurka da kasarsa za ta dore duk da rashin tabbas din da zaben Donald Trump ya jawo.

Da ya ke jawabi a wajen wata liyafa tare da 'yan kasuwar Amurka da China, ya ce irin sha'awar da 'yan kasuwar Amurka ke da ita ta yin kasuwanci da China bata canza ba.

Mr wang ya ce ya gamsu cewa, kamfanoni da kuma gwamnatin Amurka za su yi zabin da ya dace domin su ci moriyar kasuwannin kasar Sin.

A lokacin yakin neman zaben sa, Donald Trump ya yi amfani da kakkausan lafazi kan China, inda ya ce gwamnatin kasar na yaudarar jama'a game da darajar kudin ta, inda ya ce zai saka harajin kashi 45 cikin 100 akan hajojin da suka fito daga kasar China.