An cigaba da kai kayan agaji iyakar Jordan

Akwai 'yan gudun hijra kusan dubu 85 a iyakar Jordan

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Akwai 'yan gudun hijra kusan dubu 85 a iyakar Jordan

Bayan zazzafar tattaunawa da sojojin Jordan, majalisar dinkin duniya ta cigaba da kai kayan agaji ga 'yan gudun hijrar Syria kusan dubu tamanin da biyar wadanda yawancinsu mata ne da kananan yara ne.

Suna zaune ne a wasu sansanoni na wucin gadi guda biyu a zube a wani yanki da ke kan iyaka.

Jordan ta rufe iyakarta tun bayan wani hari da aka kai da ya yi sanadiyyar rasa rayukan sojojinta bakwai wanda kungiyar IS ta dauki alhakin kai wa.

Tun daga nan hanya daya kawai ake amfani da ita wajen kai kayan agaji da suka hadar da abinci.

Majalisar dinkin duniyar ta ce tana fata yanzu zata samu damar bude dakin shan magani ga 'yan gudun hijrar.