Trump: Ba zan gurfanar da Hillary gaban kotu ba

Donald Trump da Hillary Clinton
Bayanan hoto,

Trump dai ya taba cewa Hillary za ta kasance a gidan yari idan shi ne shugaban kasa.

Shugaban Amurka mai-jiran-gado Donald Trump ci gaba da yin watsi da tsauraran alkawuran da ya yi lokacin yakin neman zabe - inda a yanzu ya yi watsi da batun gufanar da Hillary Clinton gaban kotu kuma ya ce ba zai kafe kan ra'ayi guda ba kan batun sauyin yanayi.

A cikin wata doguwar hira da jaridar New York Times, Mr. Trump ya ce ba zai so ya bata wa iyalin Clinton rai ba, yana mai cewa shi yana son ya manta abin da ya wuce baya ne.

Da aka tambaye shi game da goyon bayan da ya samu daga kungiyar Alt-right ta masu ra'ayin rikau da masu zazzafan kishin fararen fata, Mr. Trump ya ce ya yi tir da al'amarinsu kuma bai san da zamasu ba.

Ya ce ba zai so ya ba kungiyar da ta kunshi masu ra'ayin 'yan Nazi da masu tsananin kishin farar fata da kuma masu kyamar Yahudawa kwarin gwiwa ba.