'Facebook zai ba China damar tace bayanai a shafinsa'

Mark Zuckerberg a China

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Facebook dai na fafutukar kara yawan masu mu'amala da shi a duniya

Wani rahoto da jaridar New York Times ta wallafa ya ce shafin sada zumunta na Facebook na tsara wata sabuwar manhaja wadda ake iya amfani da ita wajen hana wasu bayanai bayyana a shafukan mutane a wasu sassan duniya.

Wasu jami'an kamfanin Facebook din uku sun shaida wa jaridar cewa an tsara manhajar ne domin taimaka wa kamfanin samun karbuwa a kasar China.

Kodayake sun ce mai yiwuwa ba za yi amfani da ita ba daga karshe, wanda ya kirkiro da shafin dai Mark Zuckerberg ya kwashe lokaci mai tsawo yana hulda da shugaban kasar ta China, Xi Jinping, har ma ya daukar wa kansa koyon harshen sinanci.

Kawo yanzu dai kamfanin na facebook bai tabbatar ko musanta samar da wannan manhajar ba, amma dai ya tabbatar da cewa yana kara karantar kasar ta China.

Martani

Wata kungiyar masu kare hakkin masu amfani da shafukan internet ta bayyana samun wannan labarin a zaman ''abin damuwa matuka.''

Kungiyar ta Electronic Frontier Foundation, wadda ke fafutukar inganta kiyaye sirrin masu amfani da internet ta shaidawa BBC ta bakin wani jami'inta Eva Galperin cewa; suna yabawa ma'aikatan kamfanin na Facebook wadanda suka tsegunta wa jaridar ta New York Times wannan labari.

Rahotanni dai sun ambato Mr. Zuckerberg na umartar yaransa da su kirkiro da wata manhaja wadda za ta bai wa wani daga waje damar tace bayanan da ka iya bayyana a shafukan mutane.