Kocin Tottenham ya ce 'yan wasansa ba su da cikakkiyar ƙwarewa

Tottenham

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sau daya Tottenham ta ci wasa a matakin rukuni a bana, wanda ta doke CSKA Moscow

Kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya ce 'yan wasansa ba su da kwarewar da za su iya kai kungiyar matakin sili-ɗaya-ƙwala a gasar cin kofin zakarun Turai.

Kayen da suka sha a hannun Monaco da ci 2-1 ya zama silar fitar su daga gasar sakamakon rashin katabus din da suka rika yi tun farkon gasar.

Tun ma kafin nan, kungiyar ta sha kashi a filin wasanta na Wembley sau da dama, lamarin da ya karya lagonta.

Pochettino ya ce, "Akwai bukatar mu inganta salon wasanmu ta yadda za mu tunkari kowanne wasa a shirye tsaf."

"Tun farkon kakar wasa ta bana, na fada cewa abin da muke fama da shi shi ne matsalar salon buga wasa - yadda za mu sanya a ranmu cewa idan mun yi wasa ranar Asabar, to za mu yi ranar Talata ko Laraba."

Pochettino ya kara da cewa watakila zai kara kwararrun 'yan wasa a tawagarsa.