Kocin Leicester ya ce dole su zage dantse

Andy King da Jamie Vardy na yi wa juna murnar kai wa matakin sili-daya-kwala a gasar cin kofin zakarun Turai

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Andy King da Jamie Vardy na yi wa juna murnar kai wa matakin sili-daya-kwala a gasar cin kofin zakarun Turai

Kocin Leicester City Claudio Ranieri ya ce dole 'yan wasansa su yi amfani da irin azamar da suka nuna a gasar zakarun Turai domin hawa saman tebirin gasar Premier.

Kungiyar dai ta kai matakin 'yan rukunin 16 na karshe a gasar ta Turai bayan ta doke kungiyar Brugge ta kasar Belgium da ci 2-1 ranar Talata.

Sai dai sun sha kashi a wasa shida cikin wasa 12 da suka yi a gasar Premier, yayin da maki biyu kacal suka rage kafin a fitar da su daga gasar.

Ranieri ya ce,"Yanzu dole ne mu mayar da hankalinmu kan gasar Premier League."

Leicester ta buga wasan na ranar Talata ne yayin da take bukatar maki daya kacal ta kai matakin sili-daya-kwala, amma ta samu dukkan maki ukun da ake bukata domin kasancewa ta daya a rukunin G , inda take gaban Porto da FC Copenhagen.

Shinji Okazaki da Riyad Mahrez ne suka zura kwallayen da City ta ci, yayin da Jose Izquierdo ya ci wa Brugge tasu kwallon.