An kashe wani kusa a kungiyar Al-Qaeda

An kashe Faruq Al-Qahtani tun wata guda da ya gabata
Kungiyar Al-Qaeda ta tabbatar da cewa an kashe daya daga cikin manyan mambobinta, Farouq al-Qahtani,a wani hari ta sama da jirage marassa matuka na Amurka suka kai a arewa maso gabashin Afghanistan wata guda da ya gabata.
Ita kanta Amurkan sai a ranar biyar ga watan da muke ciki ne ta tabbatar da kashe dan kungiyar.
Kazalika kungiyar ta Al-Qaeda ta ce an kashe matarsa da yaransa ma.
Amurka dai ta saka sunan Al-Qahtani wanda dan Qatar ne amma haifaffan Saudi Arabia a cikin jerin mutanen da ta ke nema ruwa a jallo, inda ta ke zarginsa da hannu a kitsa hare-haren da za a kai a kasashen nahiyar turai da kuma Amurkan.