Amnesty ta zargi sojin Nigeria da kisan 'yan Biafra 150

Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari wanda tsohon janar din soji ne, ya yi yakin murkushe 'yan tawayen Biafra

Kungiyar kare hakki bil'adama ta Amnesty International ta zargi jami'an tsaron Nigeria da kisan akalla masu zanga-zangar lumana150 a watan Agustan bara.

Kungiyar ta ce sojojin sun yi amfani da muggan makamai wajen murkushe masu zanga-zangar da ke neman kafa kasar Biafra a kudu maso gabashin kasar.

Ta kara da cewa sojojin sun wuce gona da iri wajen kashe mutane a wurare daban-daban.

Wani mutum da aka harba a lokacin zanga-zangar ya shaida wa Amnesty cewa sojojin sun yi kokarin watsa masa acid a fuskarsa.

Rundunar sojin dai ta musanta zarge-zargen inda ta bayyana masu zanga-zangar a zaman barazana ga tsaron kasa.

Yunkurin kafa kasar ta Biafra ne dai ya haddasa yakin basasa a kasar kusan shekaru 50 da suka wuce.