Sojojin Nigeria sun caccaki Amnesty International

Amnesty International

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ba wannan ne karon farko da ake sa zare tsakanin Amnesty International da sojin Najeriya ba

Rundunar sojin Najeriya ta ce zargin da kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta yi mata na kisan mutum 150 tsakanin watan Agustan shekarar 2015 zuwa Agustan shekarar 2016 ba gaskiya ba ne.

A wata hira da kakakin rundunar sojin kasa Kanar Sani Usman Kukasheka ya yi da BBC bayan sanarwar da suka fitar kan batun, ya ce Amnesty International ta saba yin karya kan sojojin Najeriya.

Ita dai kungiyar Amnesty International ta ce mutanen da aka kashe 'yan fafutikar ganin an kafa kasar Biafra ne.

Sai dai Kanar Kukasheka ya ce masu fafutikar sun kashe mutane da dama - wadanda ba 'yan kabilarsu ba ne - a yankin kudu maso gabashin kasar a yunkurin da suke yi na tayar da zaune tsaye.

A cewarsa, "Tabbas wasu kungiyoyin da ba sa son zaman lafiya sun aikata kashe-kashe tsakanin watan Agustan shekarar 2015 zuwa watan Agustan shekarar 2016 a kudu maso gabashin Najeriya".

Ya kara da cewa "sun karkashe mutanen da suka fito daga wasu sassan kasar nan, suka kona su. Irin wadannan kashe-kashe ka iya jawo rikicin addini da yin barazana ga tsaron kasa shi ya sa rundunar soji ta tsoma baki."

'Ba sa son zaman lafiya'

Kanar kukasheka ya kara da cewa 'yan kungiyar MASSOB/IPOB da suka yi zanga-zanga a watan Mayun shekarar 2016 sun kashe 'yan sanda biyar kana suka jikkata wasu sojoji, baya ga banka wuta kan motocinsu.

Kazalika, a cewarsa, sun yin arangama da sojoji abin da ya sa wasu sojojin suka samu munanan raunuka, amma kungoyoyi iri su Amnesty ba su ce komai ba.

Kakakin rundunar sojin ta Najeriya ya ce Amnesty International da kungiyoyi irin ta na so a tayar da rikici a kasar shi ya sa suke sanya baki a aikin wanzar da zaman lafiya da sojoji ke yi.

Ya yi kira ga 'yan kasar da su daina yarda da abubuwan da kungiyoyi kamar Amnesty International ke fada a kan su, yana mai cewa suna yin wadannan maganganu ne domin a ce suna yin aikinsu.