Me ya sa aka farfaɗo da batun kafa kasar Biafra?

  • Nasidi Adamu Yahya
  • BBC Hausa
Masu fafutikar Biafra

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Amnesty International ta ce an kashe masu fafutika 150

Zarge-zargen da kungiyar Amnesty International ta yi wa sojojin Najeriya na kisan masu fafutikar kafa kasar Biafra 150 tsakanin watan Agustan shekarar 2015 zuwa watan Agustan bana, ya kara tayar da kura game da manufar son kafa kasar ta Biafra.

Nnamdi Kanu, wani dan kabilar Igbo da ke da zama a Birtaniya ne dai ya sake dago da wannan batu, yana mai cewa gwamnatin Najeriya ba ta yi wa 'yan kabilar ta su adalci wajen al'amuran da suka shafi ci gaban kasar.

Sai dai wannan fafutika ba ta yi karfi ba sai bayan zaben da aka yi wa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasar a 2015, abin da ya sa wasu ke zargin da walakin, wato goro-a-miya.

Wannan hasashe ya fito fili ne bayan da sau da dama gidan rediyon da Nnamdi Kanu ya mallaka ya rika aibata shugaban kasar da wasu kabilu da ba Igbo ba, lamarin da ya sa gwamnati ta rufe shi.

Har yanzu Mista Kanu na tsare a hannun gwamnati, inda ake masa shari'ar kan zargin cin amanar kasa, lamarin da ya musanta.

Kuma wasu na ganin cigaba da tsare shi ya taimaka wurin karuwar masu kiraye-kiraye a kafa kasar ta Biafra, wacce yunkurin kafa ta na farko ya haifar da yakin basasa kusan shekara 50 da ta wuce.

Sama da mutum miliyan biyu ne suka rasa rayukansu a lokacin da 'yan kabiyar ta Igbo suka yi bore, da dama daga cikinsu yunwa ce ta kashe su.

Shin an tauye hakkin al'umar Igbo?

Wannan tambaya ce da za a dade ba a iya amsa ta ba, saboda kusan kowacce kabila a Najeriya tana yin irin wannan zargi na tauye mata hakki.

Asalin hoton, Amnesty

Bayanan hoto,

Wannan hoton da Amnesty ta fitar ya nuna wani dan kabilar Igbo da ya ce sojoji sun zuba masa guba bayan sun harbe shi

A wata hira da Shugaba Buhari ya yi kwanakin baya, ya kalubalanci masu fafutikar da su fada masa irin rashin adalcin da ake yi musu.

Kazalika, a bayanin da ya yi lokacin da wasu masu yi wa kasa hidima suka kai masa ziyara a gidansa da ke Daura a kwanakin baya, ya bukace su da su shaida wa masu fafutikar kafa Biafra cewa "dole mu hada kai tare domin gina wannan kasar."

Sai dai masu sharhi na ganin ba irin wadannan kalamai ne za su hana fafutikar cigaba da samun gindin zama ba.

Malam Kabir Adamu, shugaban kamfanin Beacon Consulting da ke nazari kan sha'anin tsaro a Abuja, ya shaida min cewa fafutikar ta baya bayan nan ba ta da nasaba da batun tattalin arziki.

A cewarsa, "Wannan zanga-zanga ta fi kama da batun siyasa, domin kuwa akasarin mazauna kudu maso gabas, musammam matasa, 'yan jam'iyyar PDP da APGA ne, kuma suna yin wannan zanga-zanga ne saboda kayen da APC ta yi musu a zaben shekarar 2015."

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Matasa da dama ne a yankin ke goyon bayan wannan batu

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Malam Kabir ya kara da cewa rashin jan mazauna yankin a jiki bayan zaben da kuma nuna fifiko a rabon mukamai ne suka ta'azzara rikicin da 'yan fafutikar ke tayar wa.

Ya ce, "Gwamnatin Shugaba Buhari ba ta dauki matakin warware wannan matsala ba. Hasalima, maimakon Shugaba Buhari ya ja su a jiki, sai aka ambato shi yana cewa dole ya fifita wani yanki saboda shi ne ya zabe shi.

Hakan ya kaya tayar da hankalin masu fafutikar, wadanda ke ganin za a ci gaba da tauye su."

Mai sharhin ya ce za a kawo karshen wannan fafutika ne kawai idan gwamnati ta yi amfani da manyan shugabannin yankin domin kawar da fargabar da suke da ita ta tauye musu hakki.

Ya kara da cewa ya kamata gwamnati ta rika aiwatar da wasu aikace-aikace na ci gaban yankin domin nuna musu cewa ba za a yi tuya a manta da albasa ba.

Akwai bayanan da ke nuna cewa wannan yunkuri na samun goyon bayan wasu masu fada-aji a yankin ta bayan fage.

A don haka dole sai gwamnati ta shi tsaye wurin shawo kan matasan na Igbo da sauran al'umomin kasar masu irin wannan korafi, kafin a samu zaman lafiya mai dorewa.