Majalisar dinkin duniya ta zargi Burma da kisan Musulmi

Bayanan bidiyo,

Musulmin Rohingya na tserewa daga Burma

Wani babban jami'ai na majalisar dinkin duniya ya shaida wa BBC cewa gwamnatin Myanmar ko Burma tana yi wa Musulmi 'yan kabilar Rohingya tsiraru kisan kare-dangi.

Dakarun sojin kasar dai sun yi ta kisan 'yan kabilar ta Rohingya a jihar Rakhine, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa makwabciyar kasar Bangladesh, in ji John McKissick, na hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya.

Gwamnatin kasar dai ta kaddamar da hare-haren da ta ce na kawar da masu tayar da kayar baya ne da ke kai hare-hare a kan iyakarta tun watan Oktoba.

Ta musanta zargin da babban jami'n majalisar dinkin duniyar ya yi.

Jami'an gwamnatin sun ce 'yan kabilar ta Rohingya suna banka wuta kan gidajensu a jihar ta Rakhine domin su dora alhakin hakan kan gwamnati.

BBC ba za ta iya zuwa yankin domin tantance gaskiyar al'amari ba saboda an hana 'yan jarida da masu bayar da agaji shiga yankunan.

'Yan kasar ta Myanmar 'yan kabilar Buddha mafiya rinjaye suna yi wa Musulmi 'yan kabilar Rohingya, wadanda suka kai miliyan daya, kallo a matsayin bakin-haure da suka shiga kasar daga Bangladesh.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Jami'an da ke kula da kan iyaka sun tsare Musulmin Rohingya da dama

'Gaba kura baya sayaki'

Duk da yake dokokin Bangladesh ba su bai wa bakin-haure damar shiga kasar ba, amma ma'aikatar harkokin waje ta ce dubban 'yan kabilar ta Rohingya sun nemi mafaka a kasar.

Rahotanni sun ce dubban 'yan kabilar ta Rohingya na can suna taruwa a kan iyakar kasar.

Mr McKissick ya ce dole ne a fara duk wani yunkuri na magance matsalar kan "dalilan da suka kawo ta."

Ya kara da cewa sojojin Myanmar da jami'an da ke kula da kan iyakar kasar sun hada gwiwa wajen gallazawa Musulmin na kabilar Rohingya bayan an kashe jami'an da ke kula da iyaka tara a farkon watan Oktoba, lamarin da wasu ke dora alhakinsa kan masu tayar da kayar baya na Rohingya.