Nigeria ka iya fuskantar karancin abinci in ji gwamnati

Mota da lodin buhuna a Kano
Bayanan hoto,

Ana hada-hadar ne a manyan kasuwannin da ke kusa da iyakoki.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana fargabar cewa irin yadda ake fitar da kayan abincin da aka noma a bana daga kasar ka iya jefa al'ummarta cikin matsalar karancin abinci a badi.

Gwamnatin dai ta yi kiyasin cewa akalla ana fitar da hatsi cike da manyan motocin daukar kaya kimanin 500 a kowane mako zuwa wasu kasashen Afrika.

Sai dai Babban Mai Ba Shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkokin watsa labarai, Malam Garba Shehu, ya ce a yanzu gwamnatin ta fara daukar matakan shawo kan matsalar.

''Shugaban kasa ya saki kudade masu yawa ga ma'aikatar gona. Yanzu ma'aikatar ta fara saye wadannan kayan abincin ana ta laftawa a rumbuna don a ajiye.'' In ji mai magana da yawun shugaban kasar.