Colombia: Yarjeniyar zaman lafiya ta isa majalisa

Mayakan kungiyar 'yan tawayen FARC

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ba a dai ba 'yan kasar damar jefa kuri'a kan yarjejeniyar ba a wannan karon.

Gwamnatin Colombia ta mika wa majalisar dokokin kasar sabuwar yarjejeniyar zaman lafiyar da ta cimma da 'yan tawayen FARC domin samun amincewarta.

Ana sa ran majalisar ta yi muhawar kan yarjejeniyar a farkon makon gobe bayan da shugaban kasar, Juan Manuel Santos, da madugun 'yan tawayen FARC, Rodingo Lodono - wanda aka fi sani da Timochenko - suka rattaba hannu kanta a ranar Alhamis.

Da yake jawabi yayin saka hannun kan yarjejeniyar wadda aka yi wa gyaran fuska, shugaba Santos ya ce yarjejeniyar ta kunshi muradun al'ummar kasar.

Ya yi kira ga jama'ar kasar da su yi aiki tare don bai wa zaman lafiya damar samun gidin zama, abin da wasu ke ganin alama ce ta irin rashin tabbas din da ake da a fagen siyasar kasar.

Zubin yarjejeniyar na farko dai ya kasa kai labari domin jama'ar kasar sun nuna rashin amincewa da shi ta hanyar kuri'ar raba gardama bisa hujjar cewa yarjejeniyar ta yi wa 'yan tawayen sassauci kwarai.

Amma madugun 'yan adawa kuma tsohon shugaban kasar Alvaro Uribe ya ce zai jagoranci wata zanga-zangar nuna rashin amincewa da yarjejeniyar ta biyu wadda ya ce ita ma kamata ya yi a bai wa jama'ar kasar damar yin kuri'a a kanta.