Colombia: An sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Shugaban kasar ta Colombia ya ce yana fatan yarjejeniyar zata kawo karshen rikicin daka dade anayi
Bayanan hoto,

Shugaban kasar ta Colombia ya ce yana fatan yarjejeniyar zata kawo karshen rikicin daka dade anayi

Shugaban kasar Colombia, Juan Manuel Santos da na kungiyar 'yan tawayen FARC Rodrigo Londoño da akafi sani da Timochenko, sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar da aka sake yi mata bita wadda ake fatan zata kawo karshen rikicin da aka shafe shekara hamsin ana fama dashi a kasar.

An dai yi watsi da yarjejeniyar farko da aka cimma a watan daya gabata bayan an jefa kuri'a akai.

'Yan adawa dai sun ce anyi wa 'yan tawaye sassauci a yarjejeniyar.

A mako mai zuwa ne dai za a mika yarjejeniyar ga majalisar dokokin kasar inda hadakar jam'iyyun da ke mulkin kasar ke da rinjaye domin dubawa.

Bangaren 'yan adawa wanda tsohon shugaban kasar Alvaro Uribe ke jagoranta, ya ce zai shirya zanga-zanga akan tituna inda za a kalubalanci yarjejeniyar.