Sojojin Nigeria sun mamaye Zamfara

Sojoji

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mazauna Zamfara na murna da zuwa sojoji

Mazauna wasu yankuna na jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun ce an samu kwararar dakarun sojin kasar dauke da manyan makamai zuwa cikin jihar.

Mutanen da BBC ta yi hira da su sun ce ba su saba ganin yawan sojojin da aka tura jihar ba.

Hakan dai na faruwa ne kwanaki kadan bayan masu fashin shanu sun addabi jihar, lamarin da ya kai ga kashe akalla mutum 150.

Barayin shanun sun fi addabar mazauna yankin Dansadau da ke karamar hukumar Maru.

Wani mazaunin yankin, Malam Nuhu Dansadau, ya shaida wa BBC, "Mun ga kananan jiragen yaki uku - da wasu manya da motoci sama da 27 dauke da sojoji: wasu sun tafi yankin da aka kashe masu hakar zinare, wasu kuma sun tsaya a Magami da Dansadau. Mutanen yankin na cike da murna."

Da ma dai gwamnatin kasar ta sha alwashin murkusshe barayin shanun da suka addabi yankin.