Mahaukaciyar guguwa ta hallaka mutum 9 a Costa Rica

Guguwar ta lalata gidaje a garuruwa da kauyuka a Costa Rica da kudancin Nicaragua

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Guguwar ta lalata gidaje a garuruwa da kauyuka a Costa Rica da kudancin Nicaragua

Mahukunta a kasar Costa Rica sun ce akalla mutane 9 ne suka mutu sakamakon mahaukaciyar guguwa hade da ruwa da ake yiwa lakabi da suna Otto data abka wasu kasashen yankin a ranar Alhamis.

Shugaba Luis Guillermo Solis ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku daga ranar Litini.

Mahaukaciyar guguwar dai ta haddasa zabtarewar kasa a arewacin Costa Rica da kuma kudancin Nicaragua, inda ta yi kaca-kaca da gidaje fiye da 600.

Wakilin BBC ya ce ruwan sama mai karfin gaske hade da tabo sun mamaye garuruwa da kauyuka a kasashen biyu tare da kwashe wasu gadoji, lamarin daya tilastawa dubban jama'a kaura zuwa wasu sansanoni na wucin gadi.