Nigeria: Yau za a fara kada kuri'a a jihar Ondo

Yadda ake tantance masu kada kuri'a

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hukumar zabe ta sha alwashin kaucewa matsalolin da ake fuskanta a lokutan zabe, da suka hada da rashin bude runfunan zabe akan lokaci

Yau ne hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta wato INEC za ta gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo dake kudu maso yammacin kasar.

Hukumar zaben Nigeria INEC tace ta shirya tsaf dan tabbatar da an gudanar da sahihin zabe a jihar.

Haka kuma an tanadi dukkan kayan aiki da ake bukata dan gudanar da wannan aiki.

Jam'iyyu 28 ne dai za su fafata kuma hukumar zaben kasar ta ce ta kammala dukkan shirye shirye na gudanar da zaben.

Kuma zaben na jihar Ondo ya dade ya na daukar hankalin al'umar kasar, ganin irin barakar da ta kunnu kai tun wajen tsaida 'yan takara a manyan jam'iyyun siyasar kasar wato jam'iyya mai kulkin kasar APC da kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP.