Ana tattara sakamakon zabe a jihar Ondo

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar zabe ta sha alwashin kaucewa matsalolin da ake fuskanta a lokutan zabe, da suka hada da rashin bude runfunan zabe akan lokaci
Hukumar zabe mai zaman kanta a Nigeria ta ce ana ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Ondo da ke kudu maso yammacin kasar da aka gudanar a ranar Asabar.
Rahotanni sun ce masu kada kuri'a a wasu rumfunan zaben sun yi korafi na kawo na'urorin zabe wadanda basa aiki a mazabar su.
To sai dai mataimakin Daraktan yada labarai na hukumar zaben Mr Nick Dazang ya ce an samu nasara a wannan zabe duk kuwa da wasu korafe korafe da aka samu daga jama'a.
Hukumar zaben INEC ta ce za ta tabbatar an sanar da sahihin sakamakon zaben.
Jam'iyyu 28 ne dai suka fafata a zaben.
Kuma zaben na jihar Ondo ya dade yana daukar hankalin al'umar kasar, ganin irin barakar da ta kunno kai tun wajen tsayar da 'yan takara a jam'iyya APC da ta PDP.