Ra'ayi: Yajin aikin malaman makarantu a Nijar

A makon nan ne, Malaman makarantu a Jamhuriyar Nijar suka shiga wani yaji aiki na kwanaki hudu. Sun shiga yajin aikin ne saboda rashin biyansu kudaden albashi da sauran hakkokinsu na tsawon watanni. Gwamnatin Nijar din dai ta dage cewar saboda matsalar tabarbarewar tattalin arziki, ba za ta iya biyan dukanin kudaden da malaman ke bi ba. To shin ya za a bullo wa wannan batu? Yaya kuke kallon lamarin? Kuma ina mafita? Wannan shi ne batun da muka tattauna a kai kenan a filin 'Ra'ayi Riga.