An saki tsohon ministan Nigeria, Bagudu Hirse

Jam'ian tsaron Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sace-sacen mutane na dama wa jam'ian tsaron Najeriya lissafi

Barayin mutane sun saki tsohon ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Bagudu Hirse, bayan ya kwashe fiye da mako daya a hannunsu.

A makon jiya ne aka sace ministan a jihar Kaduna da ke arewacin kasar.

Wasu majiyoyi masu tushe sun shaida wa BBC cewa sai da aka bayar da kudin fansa kafin a sake shi, kodayake ba su fadi nawa aka bayar ba.

Sace-sacen jama'a don neman kudin fansa dai na ci gaba da zama wata babbar matsala a jahar Kaduna.

A kwanakin baya, wasu 'yan bindiga sun sace tsohuwar ministar Muhalli ta Najeriya Laurantia Malam tare da mijinta Mista Pious Malam.

Bayan haka ne kuma aka sace wani babban jami'i kungiyar Jama'atul Nasrul Islam tare da direbansa a hanyar su ta zuwa Kaduna daga Jos, babban birnin jihar Pilato.

A watan Yulin da ya gabata ma, an sace jami'in jakadancin Saliyo, Manjo Janar Nelson Williams a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna kodayake an sako shi bayan kwashe kwanaki a hannun wadanda suka sace shi.