Harin bam ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 20 a Somalia

'Yan sanda sun isa kasuwar da aka tada bam din

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

'Yan sanda sun isa kasuwar da aka tada bam din

Wani dan kunar bakin-wake da ya tashi bam din da ke jikinsa ya yi sanadin mutuwar akalla mutum a Mogadishu, babban birnin Somalia.

Mutumin ya tashi ban din ne a wata kasuwa da take tsakiyar ci ranar Asabar.

'Yan sanda sun shaida wa BBC cewa mutane da dama ne suka jikkata, suna masu cewa adadin wadanda suka zai iya karuwa.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, sai dai Al-Shabaab ta sha kai irin wadannan hare-hare.