Fidel Castro babban mai kama-karya ne— Trump

Donald Trump
Bayanan hoto,

Mista Donald Trump

Sabon zababben shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana Fidel Castro, tsohon shugaban Cuba da ya rasu, a matsayin mai kama karya da ya kuntata wa mutanen kasar shi.

Mista Donald Trump ya ce abin da za a tuna Fidel Castro da shi, shi ne, kuntatawa da talauci da take hakkokin mutane.

Lokacin da yake yakin neman zabe, Mista Trump ya yi barazanar lalata kyakyyawar alaka da Amurka ta sake kullawa kwanannan da Cuba.

Tunda farko, shugaba Obama na Amurkan ya ce ya so kulla zumunci da mutanen Cuba, inda ya ce gwamnatin shi ta yi aiki tukuru don dinke barakar dake tsakanin kasashen biyu.

Asalin hoton, STR/GETTY

Bayanan hoto,

Castro ya hambarar da Batista a Cuba kuma ya zaburar da masu juyin juya-hali a wasu kasashe

Shugabannin kasashen duniya da dama na ci gaba da jimamin mutuwar tsohon shugaban kasar Cuba, wanda ya kangare wa Amurka a lokacin yakin cacar baka, Fidel Castro.

Shugaban China Xi Jinping ya ce 'yan kasar China sun yi rashin babban aboki, yayin da shugaba Putin na Rasha ya bayyana shi a matsayin tauraron wani zamani.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ma ya ce ya yi bakin ciki da jin labarin mutuwar tsohon shugaban, dan juyin juya-hali, wanda yafi kowanne dadewa yana shugabancin Cuba.

Cikin wata sanarwa, shugaba Buhari ya bayyana Fidel Castro a matsayin zakakurin shugaba wanda ya bunkasa fannonin ilimi da kiwon lafiya da wasanni, da har wasu kasashen duniya ke cin moriyarsu.

Ya kuma bayyana shi a matsayin babban abokin nahiyar Afirka, wanda ya bayar da gagarumar gudun muwa wajen neman 'yan cin kasashen nahiyar.

A wata hira da BBC, fitaccen mai sharhi kan harkokin yau da kullun a Najeriya, Mahmud Jega, ya ce marigayi Fidel Castro ne mutumin da ya fi kowanne bai wa nahiyar Afirka taimako na samun 'yanci:

Bayanan sauti

Fidel Castro yafi kowa taka rawa a 'yancin Afirka— Jega

Shi ma Paparoma Francis ya bayyana mutuwar Fidel Castro a matsayin wani abin bakin ciki, sannan ya yi mushi addu'o'i.

Shugaba Jocob Zuma na Afirka ta Kudu ma ya bayyana marigayin a matsayin mutumin da ya yi tsayuwar daka don tabbatar da 'yan cin wadanda ake dannewa a fadin duniya.