Falcons ta kai wasan daf da karshe

Women African Cup of nation

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Super Falcons ta ci kofin nahiyar Afirka har sau tara

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta mata ta kai wasan daf da karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka, bayan da ta doke ta Kenya da ci 4-0 a ranar Asabar a Kamaru.

Haka ita ma Ghana ta kai wasan daf da karshen, bayan da ta ci Mali 3-1 a daya wasan rukuni na biyu da suka fafata.

Da wannan sakamakon Super Falcons wadda ta lashe kofin Afirka sau tara ta hada maki bakwai a rukuni na biyun.

Ita ma Ghana wadda ba ta taba daukar kofin nahiyar Afirka, ta hada maki bakwai a wasanni ukun da ta yi.

Mali ce ta yi ta uku da maki uku, yayin da Kenya wadda wannan ce gasar farko da ta fara shiga ta kare ba ta da maki ko daya.