Shugaba Hadi na Yemen ya isa Aden bayan watanni 14

Yemen

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaban Yemen Abdrabbuh Mansour Hadi

Shugaban Yemen, Abdrabbuh Mansour Hadi ya kai wata ziyara ta bazata birnin Aden dake kudanci, a karon farko cikin watanni goma sha hudu.

Birnin, ya kasance shedkwatar gwamnatin shugaba Mansour Hadi, tun bayan da 'yan tawayen Houthi suka karbe iko da babban birnin kasar, Sanaa, shekaru biyu da suka wuce, suka kuma tilasta wa shugaban tserewa zuwa Saudiya.

Dakarun kawance da Saudiya ke jagoranta sun yi ta lugudan wuta kan 'yan tawayen Houthin tun a watan Maris na bara, domin taimaka ma Mista Hadi.

Ana sa rai shugaban zai gana da jakadan majalisar dinkin duniya na musanman a Yemen a Aden a ranar Litinin.