Faransa: Jam'iyyar Republican zata yi zaben fidda gwani

Wasu masu sharhi na cewa manufofin Francois Fillon da Alain Juppe basu da bambanci

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Wasu masu sharhi na cewa manufofin Francois Fillon da Alain Juppe basu da bambanci

A kasar Faransa, yau ne 'ya'yan jam'iyyar Republican za su fidda dan takaran shugaban kasa na jam'iyyar tsakanin wasu tsofaffin Firai Ministocin kasar biyu da za su fafata.

Ana kallon Francois Fillon a matsayin dan takaran daya fi samun magoya baya, bayan nasarar daya samu a zagayen farko na zaben fidda gwanin.

Abokin takarar sa Alain Juppé, ya soki manufofin Mr Fillon, yayin da a nasa bangaren Mr Fillon ya bayyana Mr Juppé a matsayin mutumin da bai da ƙwakwarar manufa ta kawo sauyi.

Ana kyautata zaton cewa duk wanda ya lashe zaben shine zai kasance sabon shugaban ƙasar bayan da ƙuri'ar jin ra'ayoyin jama'a ta nuna cewa jam'iyya mai mulki ta 'yan gurguzu bata da farin jini sosai a Faransa.