'Bankin Musulinci na ci gaba da karbuwa a Nigeria'
'Bankin Musulinci na ci gaba da karbuwa a Nigeria'
Manajan Daraktan bankin na Ja'iz na Musulinci a Najeriya ya ce sun samu gagarumar karbuwa a wajen al'uma, ciki har da wadanda ba Musulmi ba.
Malam Hassan Usman ya shaida wa BBC cewa shekara biyar da suka wuce suka bude bankin inda suke da rassa uku kacal, amma a yanzu haka suna da rassa fiye da 27 a duk fadin kasar.
Babban jami'in bankin na Ja'iz ya kara da cewa, "haka kuma a lokacin da muka fara muna da dukiyar banki da ba ta wuce N11bn ba, amma yanzu muna da sama da N60bn."