Sojojin Syria sun kwace wani yanki na Aleppo

Aleppo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Farar-hula na tsere wa daga yankin

Rundunar sojin Syria ta ce dakarunta sun sake kwace wuri na biyu da ke hannun 'yan tawaye a gabashin birnin Aleppo.

Rundunar ta ce dakarun da abokansu sun "kama yankin Jabal Badro gaba daya".

Sa'o'i da dama kafin hakan, wasu majiyoyin 'yan tawaye sun tabbatar cewa dakarun gwamnatin sun kwace lardin Hanano da ke da makwabtaka da Jabal Badro daga hannunsu.

Daruruwan farar-hula na ci gaba da tsere wa zuwa yankunan da ke hannun dakarun gwamnati a yayin da sojoji ke ci gaba da mazaya wa zuwa gabashin Aleppo.

Yau kwana 13 kenan da dakarun na Syria suka kaddamar da yakin sake kwace yankin gabashin Aleppo - wurin da sama da mutum 275,000 ke zaune.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Syrian Observatory for Human Rights - wacce ke da hedikwata a Birtaniya - ta ce an kashe farar-hula 219, ciki har da kananan yara 27 tun da aka kaddamar da hare-haren.