An kama Sarki a Uganda kan zargin ba 'yan bindiga mafaka

map

'Yan sanda a yammacin Uganda sun kama sarkin Rwenzururu saboda wata tarzoma tsakanin jami'an tsaro da wasu 'yan bindiga da ta yi sanadiyar mutuwar mutane hamsin da biyar.

Ana zargin sarkin, Charles Wesley Mumbere da haddasa tarzomar, bayan wasu rahotanni sun ce 'yan bindigan sun kai hari kan wani ofishin 'yan sanda a garinshi Kasese.

Jami'an tsaro sun danna cikin fadar shi, lokacin da ake jita-jitar yana boye wasu 'yan bindigan.

Sarkin dai ya musanta cewa yana da hannu a cikin rikicin.

Akalla 'yan sanda goma sha hudu da 'yan bindiga arba'in da daya ne suka mutu a tarzomar.

Wani kakakin gwamnatin Ugandan, Shaban Bantariza ya zargi 'yan bindigan da yunkurin neman ballewa daga Uganda.

"'Yan bindigar sun kafa sansanoni a tsaunukan Rwenzori, a inda suke samun horo, sannan su shiga gari suna kai hari kan ma'aikatun gwamnati," Inji Shaban Bantariza.

Garin da masarautar Charles Wesley Mumbere take, Bakonzo ya na wata iyaka ne da Jamhuriyar Dimukradiyar Congo, kuma garin ya dade yana sa'insa da babbar masarautar Toro yankin.

A tsakanin watan Fabrairu da Maris na wannan shekarar, an kashe fiye da mutane hamsin a rikice-rikice tsakanin jami'an tsaro da 'yan tawaye.