Iran za ta daure dan Ayatollah Montazeri

Iran

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Masu fafituka na zargin Iran da take hakkin bil'adama

An yanke wa dan-dan daya daga cikin jiga-jigan juyin juya-hali a Iran hukuncin daurin shekaru shida, saboda ya saki wani faifan murya na mahaifinsa.

A cikin faifan dai mahaifinsa ya yi Allah-wadai da yadda gwamnati ke karkashe fursinonin siyasa.

Kafofin yada labarai na kasar sun ce an samu Ahmad Montazeri da laifin yin barazana ga tsaron kasa, da yada farfaganda.

A watan Agusta ne, Mista Montazeri ya fitar da muryar, inda aka ji mahaifin na shi, Ayatollah Hossein Ali Montazeri, ya na sukar yadda aka kashe dubban firsinoni a 1988.

An raba Ayatollah Montazeri da mukaminsa saboda Allah wadai da kashe-kashen da ya yi, kuma ya ci gaba da zama gaba-gaba wajen nuna adawa har zuwa mutuwar shi a 2009.