Francois Fillon ya lashe zabe a Faransa

Asalin hoton, AFP
Mr Fillon ya ce abun da al'ummar Faransa ke bukata shi ne gaskiya da kuma aiki tukuru
Tsohon Firai ministan kasar Faransa Francois Fillon ya lashe zaben fidda gwani na takaran shugabancin kasar karkashin inuwar Jamiyyar Republican.
Ya samu gagarumar nasara inda ya lashe zaben da fiye da kashi sittin da takwas cikin dari na kuri'un da aka kada.
Da yake jawabi ga dimbin magoya bayan sa, Mr Fillon ya yi alkawarin samar da kyakkawar yanayi ga jama'a, yana mai cewa zai sauya yadda ake shugabancin al'ummar Faransa.
Tuni dai abokin takaran sa Alain Juppe ya amince da shan kaye, inda ya yi alkawarin goyon bayan Mr Fillon domin samun nasara a babban zaben kasar da za'a gudanar shekara mai zuwa.
Ana kyautata zaton cewa duk wanda ya lashe zaben shine zai kasance sabon shugaban ƙasar bayan da ƙuri'ar jin ra'ayoyin jama'a ta nuna cewa jam'iyya mai mulki ta 'yan gurguzu bata da farin jini sosai a Faransa.

Za a tafi zagaye na biyu a zaben fidda gwani
Tsofaffin Firaiministan kasar Faransa biyu za su fuskanci juna a zaben fidda gwani zagaye na biyu na tsayar da dan takara a zaben shugaban kasar da za'a gudanar shekara mai zuwa.