Ana fuskantar fari a wasu yankunan Nijar

Yaro a cikin gona

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rashin kyawun damina na daga cikin matsalolin da manoma ke fuskanta a jamhuriyar Nijar

A Jamhuriyar Nijar wasu 'yan majalisar dokokin kasar sun nuna fargabarsu dangane da yadda daminar bana ta kasance ta fannin amfanin gona.

Yankuna da dama na Nijar dai ka iya fuskantar ƙarancin abinci, lamarin da ya sa wasu 'yan majalisar dokokin kira ga gwamnati ta fara nazarin matakan da suka dace ta dauka.

Jamhuriyar Nijar dai na daga cikin ƙasashen yankin Sahel da a kowace shekara kan fuskanci ƙarancin abinci a wasu yankunan, sakamakon ƙarancin ruwan sama ko kuma fari da ƙwari masu bata kayan noma.

Hukumomin yankin sun bayyana cewa an yi feshin maganin kwari fiye da sau uku, amma lamarin ya ci tura.

Manoma da suka shuka Wake da Gyada amma kuma kwari sun lalata su, dan haka yanzu filin gonakin kadai ake gani babu shuka a ciki.

Madam Barka Gaishatu, 'yar majalisa ce da ta fito daga yankin Dakwaro ta shaidawa BBC cewa ya kamata hukumomi su dauki matakin saukakawa jama'a ta hanyar saida musu Hatsi cikin sassaukan farashi.