Dakarun Syria sun kwato gundumar Sakhour a birnin Aleppo

Syria Aleppo

Asalin hoton, EPA/SANA

Bayanan hoto,

A cikin karshen mako dakarun Syrian suka kwace yankin Masaken Hanano

Dakarun gwamnatin Syria sun kwato gundumar Sakhour, yanki mai matukar muhimmanci a gabashin birnin Aleppo, daga hannun 'yan tawaye.

Hakan ya rage karfin wuraren da mayakan 'yan tawayen ke rike da iko a birnin na Aleppo.

Gidan talabijin na kasar da kungiyar da ke sa' ido kan hakkin bil'adama a kasar Syria sun ce gundumar Sakhour ta fada hannun dakarun kasar Syria.

A cikin watan Satumba ne Sojojin Syria da aminansu suka kaddamar da gagarumin farmakin sake kwato ikon birnin na Aleppo.

Dubunnan fararen hula sun tsere daga gundumomin gabashin Aleppo da ke hannun 'yan tawaye bayan makonnin da aka shafe ana gwabza fada.

Daruruwan iyalai ne dai suka rasa mutsugunansu a yankin da aka yi wa kawanya.