Afirka ta Kudu: Shugaba Zuma ya shiga tsaka mai wuya

Jacob Zuma

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A baya jam'iyar ANC ta sha kare Zuma daga kuri'ar yanke kaunar

Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma na fuskantar kalubale kan kuri'ar yanke kauna daga shugabannin jam'iyarsa ta ANC.

Ya sha tsallake irin wadannan kuri'un majalisar dattawa a lokuta da dama, amma wannan shi ne karon farkoda jam'iyar ANC ke tattaunawa game da matsayinsa.

Jam'iyar ta ANC ta dage zaman tattaunawarta game da muhawara kan kudirin, wanda ministan harkokin yawon bude ido Derek Hanekom ya gabatar.

Mr Zuma ya kara fuskantar matsin lamba kan zargin cin hanci da rashawa, inda rahotannin baya-bayan nan ke nuna yadda yake da alaka da iyalan attajiri Gupta.