India: Zanga-zanga kan haramta amfani da takardun kudi

India Delhi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An gudanar da zanga-zanga kan matakin a Delhi babban birnin kasar ta India

Gwamman mutane sun fito zanga-zanga a manyan biranen kasar India da dama, domin nuna adawa da matakin gwamnati na haramta amfani da manyan takardun kudi biyu na kasar.

A farkon wannan watan ne gwamnati ta sanar da haramta amfani da takardun kudin rupee na 500 da 1,000, al'amarin da ya haddasa rudani yayin da mutane suka rika jan dogayen layuka a bankuna don sauya tsofaffin kudadensu.

Fira Minista Narendra Modi ya kare matakin da cewa hakan zai rage matsalar cin hanci a kasar.

Amma jam'iyun adawa sun soko matakin.

A makon jiya ne suka dakatar da duk wasu harkoki a majalisar dokoki, kana suka bukaci Mr Modi ya nemi afuwa kan daukar wannan mataki.

Masu aiko da rahotanni sun ce babu tabbaci kan yawan mutanen da za su fita zanga-zangar, yayin da 'yan kasar ta India da dama ne suka goyi bayan matakin, duk da cikas din da hakan ya haifar musu.