Trump: Miliyoyi sun kada kuri'unsu ta haramtacciyar hanya

Donald Trump

Asalin hoton, AFP/Getty Image

Bayanan hoto,

Trump bai bada wata shaidar da ke kare ikirarin na shi ba

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce, ya samu galaba a kuri'un gama gari a ranar 8 ga watan Nuwamba, ''idan ka cire kuri'un da miliyoyin jama'a suka kada ta haramtacciyar hanya."

Trump na jam'iyar Republican, wanda ya samu galaba a duka kuri'un da aka kada a kirgen da aka yi a manyan mazabu, bai bada wata shaidar da ke kare ikirarin na shi ba.

Hakan na zuwa bayan da magoya bayan abokiyar karawarsa Hillary Clinton ta jam'iyar Democrat, suka ce za su goyi bayan sake kirgen kuri'u a Wisconsin da wani dan jam'iyar Green Party ya shige gaba.

Mrs Clinton ta samu kuri'u miliyan biyu, fiye da Mr Trump a zaben gama gari.

Amma kuma Mr Trump ya yi zarra a adadin kuri'u 270 na babbar mazabar da ake bukata don zama shugaban kasa.

Wannan ya dagora ne ga takarar da aka yi daga jiha-zuwa-jiha.